ABNA24 : Wannan furuci na Macron dai yana zuwa ne a daidai lokacin da yake kokarin sanya sharuddansa a kan Iran danganec da batun shirinta na nukiliya, da kuma batun ake yi na yiwuwar komawar Amurka a cikin wanann yarjejeniya.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran Hussain Amir Abdullahian ya bayyana cewa, Macron ko waninsa, ba su da hurumin saka Saudiyya ko wat akasa ta daban a cikin batun shirin Iran na nukiliya, bangarorin da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya ne kawai suke da hakkin yin duk wata tattaunawa, shi ma a kan abin da aka rattaba hannu a kansa a baya kawai.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawd Zarif ya mayar da nasa martanin da cewa, Macron ya manta yadda aka kulla yarjejeniya kan shirin Iran an nukilya, amma ya kamata ya kwana da sanin cewa Iran ba za ta karbi wani bangare a cikin duk wata tattaunawa da ta shafi shirin nata ba.
Haka nan kuma Zarif ya kara da cewa, dangane da batun tattaunawa a tsakanin kasashen yankin gabas ta tsakiya kuwa, tun kafin wannan lokacin Iran ta sha nanata wannan bukata, kuma ta kirayi Saudiyya da sauran kasashen yankin zuwa ga tattaunawa, amma tasirin Amurka a kansu ne ya hana yin hakan.
342/